Zababben gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya ce, gwamnatinsa za ta kasance bisa tsarin adalci da tausayi.
Namadi ya bayyana hakan ne a sakonsa na Eid el-Fitr ga jihar, mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai na ofishin mataimakin gwamna, Ahmed Haruna.
Ya mika sakon gaisuwar sa ga al’ummar jihar Jigawa tare da addu’ar Allah ya kara masa lafiya da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da Najeriya baki daya.
Ya ce watan Ramadan lokaci ne na tunani da godiya da sabunta imani don haka ya bukaci al’ummar musulmi da su ci gaba da kiyaye kyawawan darussa da suka koya.
Namadi ya jaddada kudirinsa na hada kai da daukacin al’ummar jihar, ba tare da la’akari da siyasarsu ba, wajen gina jihar da za ta zama abin alfahari ga al’ummarta.
Ya kuma yi wa al’ummar jihar murnar zagayowar wannan rana ta Idin karamar Sallah tare da addu’ar Allah SWT ya karbi ibadun su ya kuma shiryar da su kan tafarkin gaskiya.


