Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce ma’aikatar da ke karkashin sa za ta gina gadar sama a matsayin mafita ta dindindin don kawo karshen ambaliyar ruwa da aka saba yi a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Kamfanin dillancin labarai na NAN, ya ruwaito cewa, ministan ya bayyana haka ne a ranar Talata a ziyarar da ya kai ziyarar duba ayyukan gine-ginen da ake yi a hanyar Abuja zuwa Lokoja kwana guda bayan kaddamar da shi a ofis.
Ministan tare da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da wasu daraktoci a ma’aikatar sun ziyarci wasu wuraren aiki a kan hanyar.
A cewar ministan, hanyar Abuja zuwa Lokoja wata babbar kofa ce da ta hada yankunan kudu maso yamma, kudu maso kudu da kudu maso gabas da babban birnin tarayya da kuma arewacin kasar.
Ya ce don haka ya kamata a ba ta fifiko saboda muhimmiyar rawar da take takawa a rayuwar al’umma da tattalin arzikin kasa.
“Mun ga yankin da kodayaushe ke samun ambaliya, kuma mafita daya tilo da za a bi a kai shi ne a yi gadar sama a kan ta domin ta tashi sama da matakin ambaliya.
“Hakan zai yi aiki da gaske saboda yana da nisan kilomita 1.6 wanda zai dauki gadar sama guda biyar, ka sani, a ninka ta biyu.
“Don haka za mu ba da shawara mu mika wa shugaban kasa don ya ba mu ra’ayinsa saboda muna neman mafita ta dindindin ga matsalolinmu,” in ji shi.
Ministan, ya bukaci ’yan kwangilar da ke gudanar da aikin hanyar da su yi amfani da siminti, inda ya kara da cewa za a yi nazari tare da sake fasalin kwangilar hanyoyin.
Ya yi alkawarin isar da titunan siminti a fadin kasar nan, inda ya ce sun fi dorewa kuma za su iya wuce shekaru 50 sannan kuma ba a kula da su ba.


