Dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, ya bayar da tabbacin cewa, idan aka zabe shi a kan mulki a zaben shugaban kasa na 2023, zai yi yaki da tada kayar baya da rashin aikin yi.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wani gagarumin gangami da aka gudanar a jihar Kaduna wanda ya samu halartar dubban magoya bayan jamâiyyar APC daga shiyyar arewa maso yammacin kasar nan.
Taron ya gudana ne na shugaban kasa, Gwamna, Sanata, âyan takarar Majalisar Wakilai da na Jiha a shiyyar Arewa maso Yamma da ta kunshi jihohin Kaduna, Kano, Kebbi, Jigawa Katsina, Sokoto da Zamfara.
Tinubu ya kuma bayyana cewa, za a samar da ayyukan yi ga matasa masu yawan gaske a fadin kasar nan, inda ya ce zai farfado da noma domin samar da abinci.
“Da wadannan, ‘yan Najeriya za su samu kwanciyar hankali saboda za a samu wadatar abinci a kasar,” in ji shi.
Yayin da yake jawabi ga magoya bayan da suka fito daga shiyyar Arewa maso Yamma, Tinubu ya ce bai ji dadin rashin tsaro a jihar Kaduna musamman da ma Najeriya baki daya ba.
Ya kuma yabawa Gwamna Nasir El-Rufaâi bisa yadda jihar ke ci gaba da bunkasa ababen more rayuwa, inda ya nuna gamsuwa da sanin cewa Gwamnan yana da gogaggen mutum da zai karbi ragamar mulki daga hannun shi Uba Sani, dan takarar gwamna na jamâiyyar a jihar. .
âDukkan masu tayar da hankali, masu garkuwa da mutane, masu kashe mutane da ke damun tsaro a Kaduna da Arewacin Najeriya, ina tabbatar muku, za mu kawar da su.
âEl-Rufai ya ajiye gado a jihar Kaduna kuma ya bunkasa kudaden shiga da ake samu a cikin gida. Amma shugaban da ba shi da magajin kwarai ba shugaba ne nagari ba,â inji shi.
âUba Sani matashi ne, mai kuzari kuma mai gaskiya, kuma yakamata ya zama gwamnan jihar Kaduna.
Ya kara da cewa, “Ya kamata ku zabi dukkan ‘yan takarar APC, a kowane mukami na zabe.”
Da yake jawabi tun da farko, shugaban jamâiyyar na kasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana jin dadinsa ga alâummar jihar bisa yadda suka fito domin karbar dan takararsu na shugaban kasa.
Daga cikin manyan baki da suka halarci gangamin akwai Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, Abubakar Badaru na Jigawa, Atiku Bagudu na Kebbi, Simon Lalong na Filato, Aminu Masari na Katsina, da Bello Mohammed Mattawalle na jihar Zamfara.