Umar Sadiq ya sha alwashin dawowa da karfinsa daga raunin da ya dakatar da shi.
Sadiq dai ba zai buga sauran wasannin ba, bayan ya samu rauni a karawar da Real Sociedad ta yi a La Liga a Getafe a watan jiya.
Dan wasan na Najeriya, wanda aka yi masa tiyata kwanaki kadan, a halin yanzu yana kan aikin gyara jiki.
Dan wasan ya yi amfani da shafukan sada zumunta inda ya nuna jin dadinsa da irin goyon bayan da ya samu kawo yanzu.
“Kowace rana albarka ce da dama, kuma ina so in yi amfani da wannan damar in ce na gode da irin kauna da kulawar da kuka nuna min, a gare ni lokaci ya yi da zan huta kadan in dawo da karfi. Mafi kyawun har yanzu yana zuwa, ”in ji shi.