A Wani al’amari dake kama da amsa kira, matasan Jam’iyyar PDP a fadin ƙasa, sun kaddamar da wani shiri mai taken PDP sabon karni, a dakin taro na Shehu Musa Yar’adua dake Abuja, domin wayar da kan yan Najeriya.
A cikin mahalarta taron harda shi kan sa dan takarar shugabancin kasa, Atiku Abubakar da mataimakin sa Sanata Ifeanyi Okowa, sai shugaban Jam’iyyar, Sanata Dr Iyorchia Ayu da Boni Haruna da Liyel Imoke, tsohon gwamnan Cross River da gwamnan jihar Taraba gami da tsofaffin sanatoci da yan majalisar wakilai masu ci da kuma sauran jiga-jigan Jam’iyyar PDP.
A jawabin sa, dan takarar shugaban kasar, ya godewa matasan bisa wannan yunkuri, inda ya bukaci da su zage dantse, domin gina cigaba da hadin kan kasa. Ya jaddada bukatar samun gwamnati wadda za ta tallafawa matasa da mata, domin basu damar aiki da basirar su ga aikin gina kasa. Ya kuma yi alkawarin cewa, zai goyi bayan kwaskwarima ga kundin tsarin mulki, domin daukaka darajar ƴan kasa idan ya samu dama.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun gadinsa a ɓangaren labarai, Abdulrasheed Shehu ya sanya wa hannu ya ce, kamar yadda ya fada a yayin gangamin yakin neman zaben gwamnan jihar Osun, ya bukaci matasan su karbi katunan zaben su, kuma su shirya yin zabe tare da kare kuri’ansu.
A nasa bangaren, shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, ya godewa matasan, bisa bujuro da wannan tsari, inda ya yi kira a garesu su yi aiki tare da Wazirin Adamawa wanda ya ce, ya sanya dukiyar sa ta kashin Kai a ilimantar da matasa a dukkan matakai, kuma yana cikin wadanda suka tsara managartan manufofi kan ilimi a can baya.
Babban mai jawabi a yayin taron, Emana Ambrose Amawhe Wanda Yar’ Takarar mataimakin gwamna ce a zaben badi, ta godewa tsohon mataimakin shugaban kasar kasancewar sa Mai farfado da kyakkyawan fata ga mutane, inda tace suna tare da Atiku Abubakar saboda kyakkyawan kundin manufofin sa da kuma son sa ga tafiya tare da kowa domin zaman lafiya da fahimtar juna.
Wadanda suka shirya taron sun ce, sun kaddamar da kashin farko na tsarin a ranar 24 ga watan Afrilun bana, Inda suka ce wannan shi ne na biyu, kuma taken sa shi ne sake tsara Najeriya Wanda ke nufin sake hade kan jama’a, habaka tattalin arziki da ilimi da ingantaccen tsarin fedaraliyya . Kuma sun yi alkawarin wayar da kai da horar da yan Najeriya domin su fahimci nauyin dake kan su a matsayin su na yan kasa.