Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce, zai ci gaba da taka rawar gani ko da ya fice daga jam’iyyar PDP.
A cewarsa shugabanci abu ne na daidaiku ba tare da alaka da kowace jam’iyya ba.
Wike ya ce, idan aka ba shi dama, zai yi nasarar magance ‘yan fashi a Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wajen bikin kaddamar da titin Ogbunuabali-Eastern bypass a Ribas.
“Shugabanci ba na jam’iyya bane, shugabanci na mutum ne. Jam’iyya abin hawa ne kawai don aiwatar da burinku, don ku iya gaya wa mutanenku ‘Ina da wannan damar; Ina da wannan ingancin da zan ba ku sabis’.