Ministan Ƙwadago a Najeriya Chris Ngige ya janye daga neman takarar shugaban ƙasa da yake yi ƙarƙashin jam’iyya mai mulki ta APC, yana mai cewa zai ci gaba da aikinsa na minista.
Da yake bayyana janyewar tasa a cikin wata sanarwa ranar Juma’a a Abuja, Mista Ngige ya ce ya ɗauki matakin ne bisa kishin Najeriya.
“Na ɗauki matakin bisa kishin ƙasa don na samu damar mayar da hankali kan aikina na ci gaba da taimaka wa Shugaban Ƙasa da gwamnati…kuma da dalilai na iyalaina,” in ji sanarwar.
Ministan ya ƙara da cewa zai ƙaurace wa “shiga duk wasu shirye-shiryen APC na zaɓen 2023 tun daga kan zaɓukan fid da gwani”.
Ya ce tuni ya faɗa wa shugaban ƙasa matakin da ya ɗauka.
A jiya Juma’a ne Shugaba Buhari ya yi wa ministocinsa 10 ban-kwana da ke son tsayawa takara a muƙamai daban-daban, kuma Ngige na cikinsu. In ji BBC.