Ɗan takarar gwamnan jihar Kano ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, Mohammed Abacha, ya ce, jihar na buƙatar sabon fasalin kasuwanci na zamani, kuma ya sha alwashin kawo hakan.
Mohammed Abacha ya yi wannan iƙirari ne a lokacin muhawar ‘yan takarar gwamnan jihar da BBC ta gabatar a Jihar ranar Asabar.
Ya kuma sha alwashin tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa domin su bunƙasa jarinsu.