Paris Saint-Germain za ta kara da kungiyar Al Nassr ta Cristiano Ronaldo da Inter Milan a wasannin sada zumunta na bazara a Japan.
A bazarar da ta gabata, PSG ta je Japan don buga wasanni uku na cikin gida kuma jama’a da yawa sun yi maraba da su.
A bana za su kara da Al Nassr a Osaka ranar 25 ga watan Yuli da kuma kungiyar J-League Cerezo Osaka kwanaki uku bayan haka.
Sai dai Ronaldo ba zai yi karo da tsohon abokin hamayyarsa Lionel Messi ba, kamar yadda aka sanar da ficewar kyaftin din Argentina.
Haka kuma Messi baya cikin ‘yan wasan PSG da aka yi amfani da su wajen tallata wannan rangadi a shafin su na yanar gizo.
Sun kawo karshen ziyarar ta Japan da Inter, wacce za ta kara da Manchester City a wasan karshe na gasar zakarun Turai, a filin wasa na Tokyo na kasa a ranar 1 ga Agusta.


