fidelitybank

Zan bayyana ra’ayi na a kan dan takarar da zan marawa baya a 2023

Date:

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ce zai bayyana tare da fara yi wa ɗan takarar shugaban ƙasar da yake goyon baya yaƙin neman zaɓe a watan Janairu.

Da yake magana ranar Alhamis yayin buɗe aikin gadar sama a jihar, Wike ya ce zai jagoranci magoya bayansa zuwa jiha bayan jiha don yi wa ɗan takarar kamfe.

“Daga Janairun sabuwar shekara, zan faɗa wa mutanena wanda za su zaɓa. Saboda haka, duk mutanen da suke ta zato da kuma zagi na su jira Janairu ya zo,” in ji shi.

Tun bayan da Wike ya sha kaye a zaɓen fitar da gwani na takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, aka shiga ruɗani a jam’iyyar, inda ya fara adawa da Atiku Abubakar – wanda ya kayar da shi a zaɓen.

Daga baya Wike da wasu gwamnonin PDP biyar suka kafa wani rukuni da suke kiran kan su G5 da zimmar ci gaba da adawa da Atiku, kuma suka nemi Shugaban PDP na Ƙasa Iyorchia Ayu ya sauka daga muƙaminsa a matsayin sharaɗin sulhu.

Sai dai Mista Ayu ya ce, ba zai sauka ba “saboda ba su suka zaɓe ni ba”.

legit ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gobara na cigaba da lakume wasu yankunan Turai

Gobarar daji na ci gaba da ruruwa a sassan...

An kama Fursunoni 7 da suka tsere daga gidan kurkukun jihar Nasarawa

Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya ta ce...

Gwamnati za ta gina titin jirgi a jihohi shida

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta haɗa gwiwa da...

Tinubu ya na cikin koshin lafiya – Farouk Adamu Aliyu

Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Faruk Adamu...

Amurka ta saka ladan dala miliyan biyar a kamo jagoran ‘yandaban Haiti

Amurka ta sanya dala miliyan biyar a matsayin lada...

Gwamnati ta janye karar da ta shigar kan Fasinjar jirgin Ibom

Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar da ta shigar kan...

Na so komawa Manchester United a 2012 – Lwandowski

Ɗanwasan gaban ƙungiyar Barcelona ta Spain, Robert Lewandowski ya...

Isak ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gaba Alexander Isak ya nace sai ya bar...

Sadiq Umar da Bello El-Rufai sun sayi ƙungiyar Ranchers Bees ta Kaduna

Ɗanwasan tawagar Super Eagles ta Najeriya da Real Socieded...

Atiku zai iya guduwa daga ADC ya koma PDP idan Jonathan ya tsaya takara – Diran

Tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa,...

Zoben matar Ronaldo ya kai dala miliyan 5 – Masana

Masana sun yi kiyasin tsadar zoben da Cristiano Ronaldo...

Kama Tambuwal ya na da alaka da shigarsa cikin hadakar jam’iyya – Atiku

Tsohon ɗantakarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce kama...
X whatsapp