Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana matakan da zai dauka wajen magance matsalar wutar lantarki da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.
Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a wata sanarwar da ya fitar ranar Alhamis a Abuja babban birnin kasar.
Ya ce, abu na farko da zai yi idan ya hau mulki shi ne zai cire damar da gwamnatin tarayya ce kadai ke da ita ta samar da wutar lantarki ya bai wa jihohi damar su rinka samar da wutar lantarkinsu su ma.
Atiku ya kara da cewa, mafita ta biyu kuma bayan wannan ita ce kafin karin samun wutar lantarki sai an inganta hanyoyin rarrabata ta hanyar hadin gwiwar gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
Ya ce, hakan kuma zai yi wu ne idan aka kyale gwamnatin tarayya ta mayar da hankali kan tsare-tsare da sanya ido da kuma inganta hanyoyin samar da wutar lantarkin.
Atiku ya ce, yanayin da ya ga samar da lantarki a kasar na fuskantar matsaloli a cikin sa’oi 24 da aka yi babu wutar ya sa ya fara tunanin hanyoyin da zai bi wajen samar da maslaha a wannan bangare.
Ya ce, wannan tsari nasa na kunshe a cikin wani kundin da ya tsara kan yadda zai warware matsalolin da ake fuskanta a Najeriya.


