Zababben gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi alkawarin aiwatar da tsarin dimokuradiyyar da ya dace da jama’a tare da mai da hankali kan zaman lafiya da ci gaban jihar.
A jawabinsa na karramawar da ya yi a Kaduna ranar Litinin, bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna, Sani ya yabawa al’ummar jihar bisa yadda suka ba shi da abokin takararsa shugabancin jihar.
A cewarsa, “Mun karbi wannan gata tare da babban nauyi, za mu aiwatar da umarnin dimokuradiyya na jama’a tare da mai da hankali da sadaukar da kai, za mu yi mulki domin kowa ya samu zaman lafiya da ci gaban jihar.”
Karanta Wannan: ‘Yan bindiga sun harbe liamamin masallaci a Kaduna
Ya bayyana godiyarsa ga shugabannin gargajiya, al’umma da na addini wadanda suka samar da yanayi na zaman lafiya tare da yaba wa kokarin shugabannin jam’iyyar APC a kowane mataki na namijin kokarin da suke yi.
Sanata Uba Sani ya godewa zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa sakon goyon bayan yakin neman zabensa.