Shugaban Botswana, Mokgweetsi Masisi, ya yi barazanar aika giwaye 20,000 zuwa Jamus, sakamakon takaddamar shigar da farauta daga ketare.
Ma’aikatar muhalli ta Jamus a farkon wannan shekarar ta nuna yuwuwar tsaurara kayyade shigo da kofuna na farauta saboda matsalar farauta.
Masisi ya shaidawa jaridar Bild ta Jamus cewa haramta shigo da kofunan farauta zai talauta ‘yan Botswana ne kawai.
Ya kara da cewa, kokarin kiyaye muhalli ya haifar da fashewar adadin giwayen kuma farauta wata muhimmiyar hanya ce ta kiyaye su.
Botswana ta haramta farautar ganima a shekarar 2014 amma ta dage takunkumin a shekarar 2019 sakamakon matsin lamba daga al’ummomin yankin. A yanzu kasar na fitar da kason farauta a shekara.
Garken giwaye na haddasa hasarar dukiya, suna cin amfanin gona tare da tattake mazauna yankin, kamar yadda Masisi ya shaida wa jaridar Jamus.
“Abu ne mai sauqi mu zauna a Berlin mu sami ra’ayi game da al’amuranmu a Botswana. Muna biyan farashi don adana waɗannan dabbobin ga duniya,” in ji shi.
“Ya kamata Jamusawa su zauna tare da dabbobi, kamar yadda kuke ƙoƙarin gaya mana.
“Wannan ba wasa ba ne,” in ji Masisi, wanda ƙasarsa ta ga yawan giwaye ya ƙaru zuwa kusan 130,000.
Kasar Botswana, wacce ita ce mahaifar giwaye mafi girma a duniya, ta riga ta ba da giwaye 8,000 ga Angola da kuma wasu 500 ga Mozambique, a kokarinta na magance abin da Masisi ya bayyana a matsayin “yawan yawan jama’a”.