Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce, za ta tura ƙarin dakaru, domin kyautata tsaro a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Matakin ya biyo bayan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kan jirgin ƙasa, inda suka kashe mutum aƙalla takwas da raunata wasu 41 sannan suka sace wasu da dama a yammacin Litinin da ta gabata.
Wani saƙo ɗauke da hotuna da mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna dakarun jere a kan layi.
“Dakaru sun shirya tsaf don tura su aiki na musamman a kan hanyar Abuja-Kaduna. Ana yi musu jawabi a hedikwatar ‘yan sanda ta ƙasa kafin su fita a yau Asabar,” in ji Mista Adejobi.
Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya kai ziyara wurin aikin da ake yi na gyara layin dogon da ‘yan bindigar suka ragargaza da bam a harin na ranar Litinin.