fidelitybank

Zamu yi zanga-zanga tsirara a ofishin EFCC idan ba a gaggauta sakin tsohon gwamna Obiano – Ƙungiyar mata

Date:

Wasu ƙungiyar Mata a Anambra karkashin inuwar Anambra-North Women Empowerment Movement (AWEM), sun nuna rashin jin dadinsu kan ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, inda suka sha alwashin yin zanga-zanga tsirara idan hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta ci gaba da tsare shi a gidan yari ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotun shari’a ba.

AWEM sun bayyana haka ne a lokacin da suke mayar da martani ga faifan bidiyo na Obiano a ofishin EFCC, inda aka ga tsohon gwamnan sanye da guntun wando da riga.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, shugabar kungiyar ta AWEM, Uju Ifunanya Edochie yayin da ta ke nuna rashin jin dadin ta game da ci gaba da tsare Obiano, ta yi Allah wadai da kakkausar murya da abin da ta bayyana a matsayin rikon sakainar kashi da rashin da’a wajen gudanar da shari’ar.

Ta ci gaba da cewa hukumar EFCC ba ta da tsaro idan aka yi la’akari da yadda za a iya yin faifan bidiyon wani tsohon gwamna, inda ya kamata a ce yana tsare a hannun jami’an tsaro da aikewa da jama’a a shafukan sada zumunta, domin yi wa tsohon gwamnan ba’a.

Daga nan sai kungiyar ta yi barazanar cewa za ta yi zanga-zanga tsirara a ofishin EFCC na Abuja idan EFCC ba ta gaggauta sakin tsohon gwamna Obiano ba ko kuma ta kai shi kotu.

naija hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp