Kwararrun ƴawasa daga kasashen waje za su shiga sansanin Flying Eagles da ke Abuja a mako mai zuwa domin tunkarar gasar cin kofin nahiyar Afirka na ‘yan kasa da shekaru 20.
Babban mai horar da ‘yan wasan, Ladan Bosso ya gayyaci ‘yan wasa 35 a mataki na biyu na atisayen zangon su ranar Asabar.
Bosso ya kuma bai wa ‘yan wasa hudu da ke kasar waje, Ibrahim Mohammed, Ahmed Abdulahi, Lekan Oyedele da Samson Lawal fensho a gasar.
Ana sa ran ‘yan wasan kasar za su isa Abuja ranar Litinin.
Najeriya za ta mika jerin sunayen ‘yan wasa 21 na karshe a gasar ta AFCON ta U-20 a ranar 20 ga watan Janairu.
Kungiyar ta Flying Eagles tana rukunin A ne da mai masaukin baki Masar da Mozambique da kuma Senegal.
Za a gudanar da gasar ne daga ranar 19 ga watan Fabrairu zuwa 11 ga Maris.