fidelitybank

Zamu warware matsala da ‘yan IPOB idan na hau mulki – Obi

Date:

Dan takarar shugaban kasa a Najeriya na jam’iyyar Labour Party (LP), Mr Peter Obi, ya ce, zai tattauna da ‘yan haramtacciyar kungiyar nan ta masu fafutukar neman ‘yancin Biafra (IPOB) da sauran masu fafutuka domin maido da zaman lafiya kasar, idan aka zabe shi.

Mr Obi ya bayyana hakan ne a hira ta musamman da kafofin gidan jaridar Daily Trust, a Abuja yayin da yake amsa tambaya a kan matsalar tsaro a Najeriya.

Dan takarar na jam’iyyar Labour wanda tsohon gwamnan Jihar Anambra ne, ya ce salonsa zai zama daban da na takwarorinsa kan wannan matsala idan har aka zabe shi a ranar 25 ga watan Fabrairu na shekara mai kamawa 2023.

Obi ya ce, ya sha nanatawa ba sau daya ba ba sau biyu ba, cewa Najeriya ba ta da masu fafutuka fiye da kasar Brazil.

”Idan kana so zan nuna maka kasashen da suka yi fama da masu fafutuk a baya, ko Brazil ce ko Mexico ce, ko wannan ce.

”A kudu maso gabashinmu abu ne mai sauki, zan yi tattauna, zan tattauna, dumukuradiyya ce kuma a mulkin dumukuradiyya kana mulki ne da cimma matsaya. Idan wani ya ce ba ya jin dadi, sai ka kira shi ka zauna da shi ka tattauna da shi,” in ji Mista Obi.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp