fidelitybank

Zamu tsaurara tsaro a rumbun abinci – NEMA

Date:

Hukumar kai ɗaukin gaggawa ta Najeiya (Nema) ta ce za ta tsaurar tsaro a rumbunan ajiye kayan abincinta da kuma ofisoshinta da ke faɗin Najeriya domin kare su daga ‘ɓata-gari’

Hakan na zuwa ne bayan harin da aka kai kan wani daga cikin rumbunanta da ke Abuja, babban birnin ƙasar a ranar Lahadi.

Wasu matasa ne ake zargin sun kai farmaki kan rumbun wanda ke unguwar Gwagwa da ke birnin na Abuja, inda suka yi awon-gaba da kayan abinci da kuma sauran abubuwan da aka taskace a rmbun.

Wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun hukumar ta NEMA, Manzo Ezekie, ta ce “Shugaban hukumar na ƙasa, Mustapha Ahmed ya bayar da umarnin a tsaurara tsaro a ofososhi da kuma rumbunan ajiye kayan hukumar a faɗin Najeriya domin kauce wa kutsawa cikin su.”

Najeriya dai na fama da matsi na tattalin arziƙi, inda mutane da dama ke kokawa kan rashin abinci da tsadar kayan masarufi.

Kafin fasa rumbun ajiye abincin a Abuja, an samu rahotannin yadda mutane suka far wa motocin dakon kayan abinci tare da yin wawason abin da suke ɗauke da shi a wasu sassan ƙasar.

Ko a makon da ya gabata kungiyar ƙwadago ta ƙasar (NLC) ta gudanar da wata zanga-zangar yini ɗaya a ƙasar domin matsa wa gwamnati lamba kan ta ɗauki matakan da suka dace wajen kawo sauƙi ga matsalar rayuwa da al’umma ke ciki.

Gwamnatin ƙasar dai ta ce ta fito da tsarin raba kayan tallafi ga al’umma da kuma bai wa masu ƙaramin ƙarfi tallafin kuɗaɗe.

uanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp