Babbar ƙungiyar ɗalibai a kasa NANS ta ce, za ta fara gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya idan malaman jami’a ba su sasanta da gwamnatin ba, domin janye yajin aikin da suka shiga na wata ɗaya.
Mataimakin Shugaban NANS, Yazeed Tanko Muhammad ya shaidawa BBC cewa, za su rufe dukkan titunan da ke shiga birnin Abuja daga ranar Litinin mai zuwa idan ba a janye yajin aikin ba.
“Zanga-zanga ce da idan muka fara ta ba za mu daina ba har sai malamai sun dawo bakin aiki, har sai mun samu mafita,” in ji shi.
“Muna kira ga shugaban ƙasa da shi ma ya nuna mana goyon baya ya zauna a gida, kar ya je aiki ranar Litinin ɗin.”
A farkon makon da ya gabata ne ƙungiyar ASUU ta malaman jami’ar ta fara yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya bayan ta zargi gwamnatin tarayya da rashin mutunta yarjejeniyar da suka ƙulla tun a 2009 da kuma sabuwa a 2020.