Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya rufe taron ƙawancen a Madrid, yana mai cewa matakan da aka amince za su taimaka wajen tunkarar barazanar tsaro mafi girma a shekaru da dama.
Mista Stoltenberg ya ce, mambobin Nato sun amince da tabbatar da nasarar Ukraine a matsayin kasa mai cin gashin kanta a Turai, tare da hana shugaba Putin, abin da ya kira yaƙin da yake yi.
Ya ce ƙawancen ya yi maraba ƙasashen Finland da Sweden a matsayin mambobi, ya kuma ce Nato ta shirya tunkarar duk wata ba-zata – wato yana nufin daga Rasha.
Mista Stoltenberg ya ce, mun haɗa kan mu a kan muhimman batutuwa, domin kare junanmu Ƙara yawan dakarun Nato na cikin manyan abubuwan da aka amince a taron na Madrid.
Taron ya kuma tattauna batun matsalar samar da abinci da ake fuskanta.