Gwamnatin Amurka ta yi alkawarin taimakawa Najeriya, wajen cafke wadanda suka kashe jami’anta da ‘yan sanda biyu a Anambra.
Wasu gungun wasu da ba a san ko su waye ba a ranar Talata sun kai hari kan ayarin motocin gwamnatin Amurka biyu a karamar hukumar Ogbaru.
ayarin motocin na dauke da ‘yan Najeriya 9 da ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka biyar da kuma jami’an ‘yan sandan Najeriya hudu.
Tawagar ta yi tattaki ne gabanin wata ziyarar da ta shirya kai wa wani aikin shawo kan ambaliyar ruwa a Anambra wanda gwamnatin Amurka ta dauki nauyi.
A wata sanarwa da ofishin jakadancin ya fitar a daren Laraba ta ruwaito sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken yana cewa har yanzu Amurka ba ta san dalilin kai harin ba da kuma ko an kai harin ne kan Ofishin Jakadancin.
“Maharani sun kashe akalla mutane hudu daga cikin ayarin motocin. Hukumomin Amurka na hada kai da takwarorinsu na Najeriya domin sanin wurin da wadanda lamarin ya shafa ba a san inda suke ba.
“Muna yin Allah wadai da wannan harin. Za mu yi aiki kafada da kafada da takwarorinmu na jami’an tsaron Najeriya wajen neman gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban kuliya, “in ji Blinken.
Amurka ta ce ba ta da fifiko fiye da tsaro da tsaron jami’anta, tana mai jajantawa iyalan wadanda aka kashe a harin.
Sanarwar ta kuma kara jaddada aniyar Amurka ga al’ummar Najeriya na taimakawa wajen yaki da tashe-tashen hankula da rashin tsaro.