fidelitybank

Zamu tabbatar ba sunayen bogi a masu zabe – Jam’iyyu

Date:

Jam’iyyu na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu, tun bayan gabatar musu da kundin rijistar masu zaɓe da Hukumar zabe ta kasar, INEC ta yi a ranar Laraba.

Cikin adadin masu zaɓe sama da miliyan 93 da kundin rijistar ya ƙunsa, maza ne suka fi yawa inda suka kai sama da miliyan 49, sai mata su kuma sama da miliyan 44.

Injiniya Yabagi Sani shi ne shugaban kwamitin tuntuɓa tsakanin jam’iyyu wato IPAC.

Ya ce dokar zabe ta kasa ta tilastawa hukumar zaben ta mika wa dukkan jam’iyyun siyasa na kasar kundin rajistar masu zaben da ta hada.

“Wannan zai ba jam’iyyu damar sanin inda wadanda aka yi wa rajista suke, da inda za a same su. Kan haka ne jam’iyyun za su iya sanin adadin wadanda suka yi rajistar da inda za iya samunsu.”

Ya ce bayan sun karbi rajistar zaben, jam’iyyun siyasar za su gudanar da bincike kan wadanda ke da katin zabe wato PVC da ‘yan jam’iyyar da ba su da katin samsam. In ji BBC.

Kan ko jam’iyyun siyasar sun gamsu da kundin masu rajistar, Injinaya Yabagi ya ce a baya akwai damuwa cewa rajistar zaben ta kunshi sunayen wasu mutane na bogi, amma bayan an gudanar da bincike mai zurfi, an gano ba haka lamarin yake ba.

“Wannan duka babu kurakurai yanzu. In dai Allah yasa INEC ta yi aiki da wannan rajistar kamar yadda aka tsara, da kuma yadda suka yi alakawarin yi, to ina ganin zai kawo wani sauyi mai ma’ana.”

Ya yi kira ga hukumar zaben da ma jam’iyyun siyasa na Najeriya, da su tashi tsaye wajen wayar da kawunan al’ummar kasar.

“Ya kamata mu sami jama’a domin mu tabbatar sun karbi katunan zabensu daga hukumar zabe, domin wannan zai ba mu damar tabbatar da sunayen da aka wallafa a kundin zaben masu sahihanci ne, ba cushe aka yi ba.”

legit news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp