Kungiyar Daliban ta ƙasa NANS, ta bai wa jami’an tsaron kasar awa 48, wanda ya yi daidai da kwanaki biyu na su saki dalibin nan da ake zargi ya ci mutuncin matar Shugaban kasa a shafinsa na sada zumunta.
Kama Aminu Muhammad, wanda ake shirin gurfanarwa a gaban kotu anjima kadan, ya haifar da cece-kuce musamman a kafafen sada zumuntar kasar, inda da dama ke ganin rashin kyautawa da yi wa doka karan tsaye wurin tsare dalibin ba bisa ka’ida ba.
Wani kusa a kungiyar ta NANS Bashir Limanci, ya ce za su shirya zanga-zanga idan har aka ki sakin shi.
Aminu mai shekaru 23 na karatu ne a jami’ar tarayya da ke Dutse, inda ake shirye shiryen fara jarabawa.
Kawo yanzu babu martanin hukumomin tsaron kan gargadin na NANS.