Kungiyar masu dillancin man fetur ta ƙasa, IPMAN, ta janye matsayarta ta sayar da litar mai daga naira 180 zuwa sama.
A yanzu IPMAN ta ce, za ta hakura ta ci gaba da sayar da shi a kan farashin gwamnati na Naira 165.
A ganawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja, Shugaban kungiyar Chinedu Okoronkwo ya ce, hukumar PPMC ta amsa musu bukatun da suka gabatar.
A kan haka ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina fargabar fuskantar karancin man fetur a gidajen man.
Mr Okoronkwo ya kara da cewa, yanzu haka ana loda man daga Legas zuwa sauran yankunan kasar, kuma yana sa ran nan gaba kadan za a daina dogayen layuka a gidajen man a fadin kasar.
A baya IPMAN reshen jihar Legas ta bayyana cewa ba za ta iya sayar da mai kasa da naira 180 a duk lita, bayan da ta ce yanayin yadda take kashe kudi kafin sauke man a gidaje ya karu sosai.