Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta karfafa sa ido a sassa da dama na jihar, domin tabbatar da matakan tsaro wajen magance matsalar fashewar iskar gas a fadin jihar.
Kwamishinan Muhalli na jihar, Dr Kabiru Getso ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a wata hira da manema labarai kan yawaitar fashewar da aka samu a jihar.
Dr Getso ya ce a matsayin matakin gaggawa, jihar ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai duba lamarin.
“A halin da ake ciki, Ma’aikatar Muhalli za ta karfafa sa ido don dubawa da kuma fadakar da jama’a kan matakan tsaro wajen kula da iskar gas da sauran sinadarai.
“Za mu fara wayar da kan jama’a kan kafofin yada labarai da kuma wuraren da ake sarrafa iskar gas.”
“Amma dangane da haka, gwamnatin Ganduje ta tsara kudirin doka don takaita abubuwan da ke sama kuma a halin yanzu ana tantance shi a ma’aikatar shari’a ta jihar.”
Ya kuma bayyana cewa an fara aiwatar da manufar jihar kan muhalli kuma za ta ba da jagoranci ga bangaren muhalli na jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN, ya ruwaito cewa, wasu munanan fashewar iskar gas guda biyu sun afku a Kano tsakanin watan Mayu zuwa Yuni kuma an yi asarar rayuka da dukiyoyi da dama.