Gwamnatin tarayya, ta ce za ta samar da kudin tallafin man fetur da ya kai Naira tiriliyan 6.72 a shekarar 2023.
Jaridar The NationĀ a Najeriya ta ruwaito Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmed na bayyana haka a Abuja babban birnin kasar ranar Alhamis.
Hajiya Zainab ta ce gwamnati ta kiyasta cewa za ta samar da kudaden ne ta hanyoyi guda biyu kamar yadda yake kunshe a cikin kasafin kudin kasar.
A karkashin hanya ta farko, ministar ta ce ”An kiyasta cewa za a samar da tallafin tiriliyan 6.72 a shekarar 2023.
Ta kuma kara da cewa wadannan kudade kamfanin NNPC ne zai samar da su a madadin gwamnatin tarayya.