Kungiyar ‘yan kasuwar canji ta Abuja, ta ce daga ranar Alhamis za ta rufe kasuwar canji har sai abin da hali ya yi, sakamakon tsadar dala da ake fama da ita a kasar nan.
Shugaban kungiyar, Alhaji Abdullahi Dauran shi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja.
Ya ce, darajar Naira ta yi faduwar da ba a taba yi ba cikin gomman shekaru na tarihin kasar nan.
A kasuwar canji, a ranar Talata, an yi musayar naira kan kowace dala a kan N1,520 yayin da a hukumance ake sayar da dala kan N892 da N910.
Kungiyar ‘yan canji ta alakanta tashin farashin dalar da ayyukan kamfanin da ke hada-hadar kudade ta Intanet irin na Crypto da ake kira Binance.
Hakan ne ya sa kungiyar yin kira ga gwamnatin kasar nan da ta hana ‘yan Najeriya hulda da kamfanin na Binance, idan dai har ana son karyewar farashin dalar.