Gwamnatin Jihar Legas, ta ce, za ta markade baburan Achaɓa 250 da ta kwace daga hannun masu karya dokokin hanya a Jihar.
Daraktan yada labaran Hukumar Kula da Dokokin Muhalli da sauran laifuka na Jihar, Mista Gbadeyan Abdulraheem ne ya bayyana hakan, a sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Talata.
Ya kuma gargadi mahaya Achaɓa da su gujewa hawa baburan da aka haramta, da kuma bin ka’idojin tuki, domin gudun fadawa hannun hukuma.