Shugaba Muhammadu Buhari, ya shaida cewa, masu daukar doka a hannusu, mallakar makamai ta haramtacciyar hanya, da kuma ribauta daga jefa tsoro da matsalolin tsaro za su ɗanɗana kudarsu.
Shugaban na waɗannan kalamai ne a garin Wudil na jihar Kano, a bikin yaye ɗalibai ‘yan sanda da ya halarta.
Buhari ya ce gwamnatinsa, za ta ci gaba da yaƙi da munanan aƙidu da miyagun mutane, yana mai jan hankali ‘yan sanda kan mayar da hankali a ayyukansu.
Sannan ya jadada bukatar samar da ci gaba a fasaha ko kariya daga hare-haren intanet, sannan ya ce za a tarwatsa maƙiyan kasa.
Najeriya dai na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, da sace mutane domin neman kuɗin fansa.