Sabuwar gwamnatin sojin Nijar, ta ce za ta mayar da martani ba tare da bata lokaci ba ga duk wata takala ko yunkurin takala daga kasashen yammacin Afirka.
Gargadin ya zo ne kwana uku kafin karewar wa’adin da kungiyar Ecowas ta ba wa Nijar din na a dawo da kasar kan turbar tsarin mulki.
Sojojin sun ce sun soke wasu yarjejeniyoyin soji da aka kulla tsakanin Shugaba Bazoum da Faransa bayan sun karbe ikon kasar.
Jakadan Nijar a Amurka, Kiari Liman Tinguiri wanda sojojin suka kora, ya ce ”idan Nijar ta durkushe to baki dayan yankin Sahel abin ya shafa, sannan yankin zai fuskanci babbar matsala, idan kuwa har aka samu matsala a yankin to kare kasashen ma zai yi matukar wuya”.
Cikin mukalar da ya rubuta a jaridar Washington Post, Shugaba Bazoum ya ce an yi garkuwa da shi inda ya yi kira ga Amurka da ma sauran kasashen Yamma a kan su taimaka a dawo da kasar kan turbar tsarin mulki.
Ya kuma yi gargadin cewa muddin aka bari juyin mulkin kasar ya yi tasiri to hakan zai haifar da mummunan sakamako.