Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce suna da yaƙinin samun nasara a babban zaɓen 2023, duk da tarin ƙalubalen da ƙasar ke ciki musamman matsalar tsaro da matsin rayuwa.
Sanata Abdullahi Adamu ya shaida wa BBC cewa, irin waɗannan matsalolin, musamman na tsaro, ba kawai a Najeriya ake fuskantar su ba har ma da wasu ƙasashen a duniya.
Ya bayyana cewa “Ba shakka akwai taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasa, amma mai hankali ya san cewa taɓarɓarewar darajar Naira ba wai mu muka haddasa ta a nan ba, batun tsaro kuma babu wata ƙasa da za ka ce tana zaman lafiya.”
Sai dai ya ce, duk da haka gwamnati na iya ƙoƙarinta na ganin an magance matsalolin.
Najeriya dai ta shafe tsawon shekaru tana fama da ƙaruwar matsalolin tsaro a sassan ƙasar.
A cewarsa, Jam’iyyar APC na aiki ne domin samun nasara a zaɓen da ke tafe sai dai ya ce akwai mutanen da ba ƴan jam’iyyarsu ba da suke musu zagon ƙasa kan wannan ƙudirin nasu.


