Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce, za ta ladabtar da ’yan siyasar da ke daukar nauyin al’umma tare da zaburar da mabiyansu kan ayyukan rashin da’a a jihar.
Gwamnati ta ce, “yana samun sahihan rahotannin sirri da ke bayyana tsare-tsare na ‘yan siyasa da suka fusata don tallafawa da kuma zuga mabiyansu ga ayyukan da bai dace ba.”
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida ya bayyana cewa ya biyo bayan sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris wanda ya kai ga fitowa takarar gwamnan jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani.
Karanta Wannan: Gwamnatin Kwara ta jajantawa al’ummar ta bisa iftila’in ruwan sama
Kwamishinan ya bayyana cewa, duba da wadannan rahotanni, gwamnati na ci gaba da sanya ido sosai da hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar ba za ta kyale mutane ko kungiyoyin da ke yin ayyukan da za su haifar da tashe tashen hankula ba, da barazana ga rayuwa da lalata dukiyoyi, yana mai cewa za a yi amfani da cikakken nauyin dokar yadda ya kamata.
Samuel Aruwan ya sake nanata cewa dakatar da zanga-zangar tituna ko jerin gwano na nan daram domin amfanin al’ummar jihar baki daya.
Ya bukaci iyaye, masu kulawa da shugabannin al’umma da su wayar da kan jama’a a unguwanninsu da su guji amfani da mutanen da ke neman cin karensu babu babbaka don haifar da hargitsi a kan kokarin gwamnati na kiyaye muhallin da mutane za su iya gudanar da kasuwancinsu na halal.