fidelitybank

Zamu kwace lasisin bankin da ya ki bayar da sababbin kudi – Zulum

Date:

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya gargaɗi bankunan kasuwanci a jihar cewa gwamnatinsa za ta ƙwace lasisin filin duk bankin da ya gaza saka sabbin takardun naira a na’urorin cire kuɗi na ATM.

Gwamnan ya yi gargaɗin ne ranar Juma’a a birnin Maiduguri lokacin da ya kai ziyara don gane wa idonsa irin dogwayen layuka da wahalar da jama’a ke fuskanta na ƙarancin sabbin takardun kuɗin.

“Duk bankin da ba shi da niyyar cika ATM ɗinsa da sababbin takardun kuɗi don sauƙaƙa wa al’umma wahalhalu, za mu ƙwace filin gininsa nan take,” in ji gwamnan cikin wata sanarwa da kakakinsa Isa Gusau ya fitar.

Karanta Wannan: Mun karbi Naira biliyan 18.6 na gyaran titi a hannun gwamnatin tarayya – Kuros Riba

Sanarwar ta ce ran Gwamna Zulum ya ɓaci ne lokacin da ya tarar da wani dogon layin cirar kuɗi, inda ATM ɗaya ne kacal yake aiki cikin 10 da ke wurin.

“Kamar yadda kuke gani, talakawa ne kawai a kan layi…An ce wasu tun ƙarfe 3:00 na dare suke a nan, wasu ma ba su ci komai ba. Sababbin kuɗin da tsofaffin duka babu, wanda hakan ke shafar harkokin kasuwanci tare da ƙuntata wa mutane,” a cewar Zulum.

Gwamnan ya ƙara da cewa lokacin da ya je Ƙaramar Hukumar Gubio ya tarar cewa babu naira N100,000 a faɗin ƙaramar hukumar baki ɗaya na tsofaffi ko sababbin kuɗin.

vanguard newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp