fidelitybank

Zamu karbi umarnin kotu akan sauya kudi – Gwamnati

Date:

Gwamnati ta ce za ta mutunta umarnin da Kotun Kolin kasar ta bayar a kan karar da wasu gwamnonin jihohi uku suka shigar inda kotun ta sa dakatar da aiwatar da wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi na naira 200 da 500 da kuma 1,000 a yau 10 ga watan Fabarairu.

A ranar Laraba ne dai kotun ta bayar da umarnin inda ta ce a dakata da amfani da wa’adin har zuwa ranar 15 ga watan na Fabarairu lokacin da za ta yanke hukunci a kan shari’ar da gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar suna kalubalantar wa’adin.

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Najeriyar, Abubakar Malami, ne ya ce gwamnatin za ta bi umarnin a yayin wata hira da tashar talabijin ta Arise TV, a jiya Alhamis.

Sai dai ministan ya ce yana fatan idan aka koma sauraren shari’ar Kotun Kolin za ta soke wannan umarni, wato ta bar Babban bakin ya aiwatar da tsarinsa na sanya wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kudin da bankin ya sauya.

Malami ya kara da cewa kasancewar Babban Bankin wanda kusa ne a shari’ar, wanda kuma ba a sanya shi ba a cikin karar da gwamnonin suka shigar, hakan ya sa a Kotun Kolin ba ta da hurumin yanke hukunci a kan batun tun ma da farko a cewarsa.

Amma kuma ya ce gwamnati ta yanke shawarar bin umarnin Kotun Kolin ne domin mutunta doka da oda.

vgn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansani a Kebbi

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta...

Za afara rijistar masu zabe a Najeriya – INEC

Hukumar zaɓe ta INEC, ta ce, nan gaba cikin...

Ma’aikatan Jinya sun dakatar da yajin aiki a Najeriya

Ministan lafiya a Najeriya ya ce, ma'aikatan jinya da...

Izak ya na É—aukar horo bayan ya dage sai ya koma Liverpool

ÆŠanwasan gab ana Newcastle Alexander Isak na can yana...

Masu tsaigunta wa Æ´an Bindiga ne ke haddasa kashe-kashe – Gwamnan Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ce masu tsegunta wa Æ´anbindiga...

Gwamnoni ku yi wa mutanen Æ™auyika da karkara ayyuka – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci gwamnonin ƙasar nan su...

Dino Melaye ya gudu daga PDP ya faÉ—a ADC

Tsohon É—an jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma,...

Isra’ila na zargin Canada da goyon bayan Hamas – Netanyahu

Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan...

Rashin tallafin agaji ka iya dawo da Boko Haram a Najeriya – MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta...

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta...

Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi...

Dalilin da ya sa na gana da Tinubu – Kofa

ÆŠan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga...
X whatsapp