Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), ta ce, ta baza jami’an tsaro 25,225 domin rufe muhimman hanyoyin mota guda 29 a lokacin bukukuwan Ista, inda ta yi barazanar cin tarar masu ababen hawa da ke fitar da hayaki mai yawa da kuma rashin fitulu da birki mara kyau.
An kuma umarci jami’an kwamandojin da su kara kaimi tare da tabbatar da tsauraran matakai a kan masu laifuffuka kamar lodin kaya, motocin haya, da hayakin da ya wuce kima.
Hukumar ta ce, za ta sanya wa masu ababen hawa takunkumin karya kayyakin gudu, lodi fiye da kima, keta haddin taya, da kuma keta alamun fitulu, wadanda suka hada da fitulun da ba su yi aiki ba, fitilolin mota, fitilun baya da kuma birki.