Kwamandan dakarun Amurka a Turai da Afirka ya ce sun fara shirin ɗaukar matakai idan aka nemi su fice daga Nijar ciki har da neman ƙasar da za su mayar da su a yammacin Afirka, kamar yadda kafofin labaran Amurka suka ruwaito.
“Za mu kasance cikin shiri idan wani abu ya faru,” a cewar Janar James Hecker yayin tattaunawarsa da manema labarai ta intanet a ranar Juma’a.
“Akwai matakai da za mu iya ɗauka da yawa idan za mu fice [daga Nijar]. Dole ne dai mu zama a shirye don ɗaukar dukkan matakan…amma muna fatan ba za ta kai ga haka ba.
“Dole za mu duba wasu ƙasashen da za mu yi ƙawance da su a [yammacin] Afirka da za mu mayar da kayan aikinmu can.”
Amurka na da dakaru aƙalla 1,000 a Nijar da ke aikin yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel, kuma har yanzu ba ta ayyana kifar da gwamnatin Bazoum a matsayin juyin mulki ba.
Da zarar Amurka ta ayyana lamarin a matsayin juyin mulki, hakan zai shafi alaƙarta da Nijar kai-tsaye, abin da ka iya kawo ƙarshen tallafin da take bai wa ƙasar da kuma zaman dakarun nata a can.