Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana kudurinsa na kara zurfafa dimokaradiyya a kasar nan tare da kafa misali mai kyau ga sauran kasashen Afirka ta hanyar tabbatar da sahihin zabe a 2023.
Buhari ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja, a wajen bukin ranar ‘yan kasashen waje na Najeriya karo na 16 na shekarar 2022, kuma karo na 4 da hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) za ta shirya.
Ranar, wadda ake bikin ranar 25 ga watan Yuli, kowace shekara, tana da taken: Hidimar Al’umma a Zamani masu Kalubalantar Duniya don Ci gaban Kasa.
Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan sa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya ce nasarar dimokuradiyyar Najeriya za ta hana hanyoyin samun sauyin gwamnati da bai dace ba a yankin da sauran sassan nahiyar Afirka.
A cikin shekara guda ne nahiyar Afirka ta shaida yadda sojoji suka mamaye kasashen Chadi, Mali, Guinea Bissa, Burkina Faso da Sudan.
Buhari ya ce: “Kamar yadda kuka sani cewa shirye-shiryen zabukan kasarmu na 2023 sun ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali kuma sun yi daidai da dokokin kasarmu da tsarin mulkinmu.
“Na sha ba da tabbacin kuduri na na kashin kaina, da na gwamnatina na tabbatar da cewa al’amura sun ci gaba da kasancewa a bayyane, a yi sahihanci, da tabbatar da gaskiya da adalci, wanda zai kai ga gudanar da zabe cikin lumana, da mika mulki ga gwamnati mai zuwa. .