Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, ya ce, za a tuna da marigayiya Sarauniya Elizabeth ta biyu, bisa jajircewarta da kuma kawo sauyi a cikin al’ummar kasar baki daya.
Sanwo-Olu ya bayyana haka ne a wajen taron tunawa da marigayiya Sarauniya, wanda aka gudanar a gidan Ikoyi na mataimakiyar babban kwamishina ta Burtaniya a ranar Laraba.
Ya ce sarauniyar ta kasance mai tawali’u kuma tana yi wa jama’a hidima da mutunci.
“Rayuwar sarauniya ta kasance mai tawali’u, mutunci da kuma alheri mai yawa domin ta kasance mai himma a duk abin da ta yi a shekarunta na hidima.
“Ban taba haduwa da sarauniyar da kaina ba sai kallo daga nesa, kuma za ku ga wata mace mai alheri wacce ta gina gadoji da sauya rayuwa a cikin al’ummar kasar baki daya.
“Ta karawa gwamnatin Burtaniya karfi da girma fiye da yadda take a yanzu, bayan da ta mika wa firayim minista 15 ta kuma ziyarci kasashe sama da 117 ciki har da Najeriya.
“Ina shakkun ko za mu sami sarki kamarta saboda shaidarta zai yi wahala ga sarauniya da sarakunan nan gaba su yi koyi da shi,” in ji shi.
Gwamnan ya ce, “Sarki na da manyan takalmi da zai cika, kuma ina yi masa fatan alheri”, ya kara da cewa zai yi wahala a wannan zamani a samu wata sarauniya, kamar yadda NAN ta ruwaito.