fidelitybank

Zamu gurfanar da wadanda suka shigo Najeriya ba bisa ka’ida ba – ‘Yan sanda

Date:

‘Yan sanda a jihar Gombe, sun kama wasu mutane da ake zargi sun shigo Najeriya ba bisa ka’ida ba.

Mutanen wadanda ake zargi sun shigo daga jamhuriyar Benin su hudu da kuma wasu biyu ‘yan Najriya.

Akalla mutane 109 ne ke kwantar da hankula a rundunar ‘yan sandan jihar Gombe bisa zargin shigowa da kasar ba bisa ka’ida ba daga jamhuriyar Benin.

Da yake bayyana hakan a wani taron manema labarai, kwamishinan ‘yan sanda jihar, Ishola Babaita, ya ce an shigo da mutanen ne ta cikin wasu motocin bas guda uku daga kasar Benin, tare da goyon bayan ‘yan Najeriya masu hadin gwiwa.

Babaita ya ce, da aka yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa su mambobi ne na QNET, wani tsarin sadarwar na internet.

Ya ce, “A ranar 18 ga watan Janairun 2022, rundunar ta samu labarin cewa, motocin bas guda uku ne suka kawo wasu gungun samari 109.

Yayin da ya bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan wajen yin sana’ar ta haramtacciyar hanya, domin kuwa ya ce, za a gurfanar da duk wadanda ake zargin a gaban kuliya.

legit new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp