Gwamnatin Tarayya na shirin gurfanar da masu amfani da PolyChlorinated Biphenyl (PCBs), wanda aka fi sani da man Transformer oil, a cikin kayan abinci.
Farfesa Babajide Alloy, mai ba da shawara ga ma’aikatar muhalli ta tarayya ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wata hira da manema labarai a wajen wani taron bita a Calabar.
A cewarsa, cin abincin da aka shirya daga sinadari zai sanya jama’a su fuskanci cututtukan daji na huhu, zuciya, koda da kuma hanta.
“Da dadewa, PCBs shine ruwan sanyaya da ake amfani da shi wajen samar da wutar lantarki, har sai da duniya ta gano cewa wannan mai guba ne, kuma ana kokarin kawar da shi.