Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce, za ta fara tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki na shekarar 2023 a ranar Lahadi da tsakar rana.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan, a wani taron manema labarai kan zaben 2023 da aka yi ranar Asabar a Abuja.
Yakubu ya ce, hukumar na sa ran samun sakamako daga jihohin daga ranar Lahadi.
“Zan so in gayyace ku da tsakar rana a gobe Lahadi, domin bude cibiyar tattara sakamakon ta kasa a hukumance.
“Muna fatan zuwa gobe, muna sa ran samun wasu sakamakon zaben da za su fito daga jihohi, musamman na zaben shugaban kasa.
“Don haka, cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa za ta bude da tsakar rana,” in ji Yakubu.
Ya kara da cewa ba za a bukaci a yi wa ‘yan Najeriya jawabi ba kafin ranar Lahadi (26 ga Fabrairu), sai dai idan akwai bukatar yin hakan.