Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce, ya tattauna da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, kuma bangarorin biyu sun amince da bukatar farfado da zaman lafiya a kasarsa a yayin yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha.
Baki daya, mun amince da bukatar dawo da zaman lafiya. Mun yaba da taimakon Turkiyya a wannan tsari, ”Zelensky ya wallafa a shafinsa na Twitter a daren Litinin bayan tattaunawar.
A yayin tattaunawar, Zelensky da Erdogan sun kuma tattauna kan barazanar samar da abinci sakamakon rikicin Rasha da Ukraine da kuma hanyoyin da za a bi wajen toshe tashoshin jiragen ruwa na Ukraine.
Sun kuma tattauna hadin gwiwa a fannin tsaro.
Sanarwar da ofishin Erdogan ya fitar ta ce, Turkiyya na ba da muhimmanci ga aikin samar da amintacciyar hanya don fitar da kayayyakin amfanin gona na Ukraine ta ruwa.
Sanarwar ta ce, Turkiyya ta yi iyakacin kokarinta na ci gaba da tattaunawa tsakanin Ukraine da Rasha.
Har ila yau, ta ce a shirye Turkiyya ta ke ta ba da tallafin da ake bukata, ciki har da shiga tsakani.
Tun da farko, Erdogan ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Rasha, Vladimir Putin.