Shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar wa masu yi wa ƙasa hidima da ke da lalurar buƙata ta musamman cewa, hukumar za ta ɗauke su aikin babban zaɓen da ke tafe.
Farfesa Mahmood ya tabbatar da haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar kwamishinonin hukumar zuwa shalkwatar masu yi wa ƙasa hidima da ke Abuja babban birnin ƙasar.
INEC ki inganta alawus din masu yi wa kasa hidima – NYSC
Ya ce ”INEC hukuma ce da ke bayar da daidaito ta fuskar ɗaukar ma’aikata. Muna buƙatar bai wa ‘yan ƙasa dama ba kawai ta jefa ƙuri’a ba, har da aikin zaɓe ba tare da la’akari da yanayin da suke ba, kamar wata lalura ta musamman, za mu ba su dama wajen gudanar da aikin zabe”.
Shugaban na INEC ya kuma yaba wa hukumar yi wa ƙasa hidimar kan taimakon da take bai wa hukumar zaɓen cikin shekaru masu yawa.
Daga ƙarshe ya alƙwarta ci gaba da aiki da yarjejeniyar da ke tsakanin hukumarsa da hukumar yi wa ƙasa hidimar, tare da alƙawarta kare lafiyar masu yi wa ƙasa hidimar a lokacin gudanar da zaɓukan ƙasar.