Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, Abdulrasheed Bawa, a karshe ya bayyana cewa, hukumar na sa ido sosai kan masu neman tsayawa takara a zaben 2023.
POLITICS NIGERIA ta tuna cewa, an yi ta cece-kuce daga ‘yan Najeriya bayan da jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da farashin tikitin kuɗin takararta na shugaban kasa a 2023 a kan Naira miliyan 100.
Jama’a da dama dai sun yi kira ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ta gaggauta binciken duk wani mai neman tsayawa takara da ya biya kudin fam dinsa. Da yake mayar da martani kan wannan ci gaba a wata hira da gidan talabijin na Channels TV, Bawa ya ce;
“Idan aka zo batun sa ido kan kudaden zabe da kuma kudaden ‘yan takara, wannan yana da alaka da aikin INEC a wannan fanni amma, ba shakka muna aiki kafada da kafada da INEC da sauran hukumomin da ke da alaka a wannan fanni. don tabbatar da cewa mun bi kudin, mun san madogaran, shin halas ne ko kuma na haram ne, domin abin da ya shafe mu ke nan.”
Ya zuwa yanzu dai Bola Ahmed Tinubu da Fasto Tunde Bakara da Yemi Osinbajo da Godwin Emefiele da Ken Nnamani da Rotimi Amaechi da Ogbonnaya Onu da Emeka Nwajiuba da Ibikunle Amosun da Rochas Okorocha sun karbi fom din takarar shugaban kasa na Naira miliyan 100.