Birtaniya ta ce, za ta bai wa Ukraine ƙarin taimakon na tallafin dala biliyan 1.6.
Wannan ya ruɓanya taimakon da Birtaniya ta baUkraine sau uku, tun soma mamayar Rasha.
Mista Boris ya ce abin da Putin ya yi a wurare kamar Buka laifukan yaki ne kuma hakan ya lalata kimarsa da ta gwamnatinsa.
Mista Boris zai halarci taron shugabannin kasashen G7 a ranar Lahadi da za a tattauna da Shugaba Zelensky kan wasu karin taimakon da Ukraine ke bukata. A cewar BBC.