Gwamnatin jihar Zamfara ta kafa wani kwamitin ‘yan-sa-kai da za su taimaka wajen samar da tsaro a faɗin jihar sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan bindiga.
Gwamnatin Zamfarar ta ce, za ta zaɓo kimanin mutum 300 daga kowace karamar hukuma cikin 14 da ke jihar.
Mustafa Jafaru Kaura mai taimakawa gwamnan jihar a ɓangaren watsa labarai, ya sanar da hakan ga BBC.