fidelitybank

Zamfara: ‘Yan ta’adda sun kona mutane a mota tare da yin garkuwa da wasu

Date:

Rahotanni na nuni da cewa, akalla mutune shida a ka kashe, yayin da a ka yi garkuwa da wasu mutane da dama, bayan da ‘Yan tadda suka tare hanyar Kauran Namoda zuwa Shinkafi a Jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilin Aminiya cewa maharan sun kuma banka wa wasu daga cikin motocin da su ka tare wuta da fasinjoji a ciki, kuma ko gawarwakinsu ba a iya ganewa.

A cewarsu, akasarin maharan, wadanda yaran kasurgumin dan bindigar nan ne da aka fi sani da Turji, sun zafafa kai hare-hare a yankin a cikin ’yan kwanakin nan, tun bayan da wani harin sojojin sama ya kashe masa wata gwaggo da mijinta da kuma mayakansa da dama.

’Yan bindigar sun tare hanyar ce a daidai tsakanin Kwanar Jangeru da Moriki, wacce dama tuni matafiya su ka daina bi, saboda rashin tsaro. Babu wanda zai iya zuwa ma ya kwaso gawarwakin mutanen da a ka kashe”. inji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa.

Shi kuwa wani mazaunin yankin mai suna Mansur cewa ya yi, “Ka san harin da sojojin sama suka kai kwanan nan ne ya fusata su. Harin ya ragargaza daya daga cikin sansanonin Turji, sannan ya kashe ’yan uwansa da yaransa da dama”.

Sai dai wasu majiyoyin sun ce ’yan bindigar sun dawo da kai hare-haren ne, domIn su nuna bacin ransu da ci gaba da rufe kasuwar dabbobi ta garin Shinkafi.

An dai jiyo wasu daga cikinsu na cewa za su ci gaba da kai hare-hare a yankin har sai lokacin da aka sake bude kasuwar dabbobin.

Aminiyar ta kuma tuntubi mai magana d’yan sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce, a ba shi lokaci zai tuntuba daga bisani, ko da ya ke bai yi hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

 

 

 

 

 

www.najnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp