Gwamnatin Zamfara ta amince da mayar da sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC) na wucin gadi daga Tsafe zuwa Gusau, saboda dalilai na tsaro.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Ofishin Mataimakin Gwamna, Mista Babangida Zurmi ya fitar a Gusau ranar Litinin.
Zurmi ya bayyana cewa mataimakin gwamnan jihar, Mista Hassan Nasiha ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin babban daraktan hukumar NYSC, Brig.-Gen. MK Fadah, a gidansa dake Gusau.
Mataimakin gwamnan ya yi takaitaccen bayani kan yanayin tsaro a jihar, inda ya ce, al’amura sun samu sauki, domin jama’a na gudanar da harkokinsu na yau da kullum.