fidelitybank

Zamfara ta kori kungiyoyi masu zaman kansu daga jihar

Date:

Gwamnatin Jihar Zamfara, ta umarci dukkanin kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a jihar, su tattara i-nasu-i-nasu su fice daga jihar ba tare da bata wani lokaci ba.

Umarnin na cikin wata sanarwa ne da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Mamman Tsafe ya fitar.

Sanarwar ta zargi kungiyoyin wadanda ba na gwamnati ba da gudanar da ayyukan da ke iya kara matsalar tsaro a jihar da makwabta.

Gwamnatin ta c,e ta lura da yadda kungiyoyin suke ta karuwa a jihar inda suke gudanar da ayyukan da suka saba wa doka.

Kuma ta c,e ta lura yawancin kungiyoyin ba su yi rijista a jihar ba kamar yadda doka ta tanada.

Sanarwar ta umarci ma’aikatu da sassa da kuma hukumomin gwamnati da su daina duk wata mu’amulla da kowa ce kungiya, tare da gargadin cewa, za a hukunta duk wata hukumar gwamnati da ta yi mua’mulla da kungiyoyin.

Gwamnatin ta kuma bayar da umarni ga hukumomin tsaro da su sanya ido domin gano duk wata kungiya da ke aiki ba tare da takardar izini daga hukumar da ta dace ba, domin gurfanar da ita a gaban kotu.

www.legit.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp