Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da dage haramcin ayyukan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Zamfara (ZAROTA).
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren harkokin majalisar dokokin jihar, Lawal Hussein, a madadin sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubakar Nakwada Gusau, ta nuna cewa matakin zai fara aiki nan take.
Don haka sanarwar ta bukaci jama’a da su kasance masu bin doka da oda tare da bayar da hadin kai ga hukumar wajen gudanar da ayyukanta na tsarin mulki domin tabbatar da tsaro a kan hanya.
Idan dai za a iya tunawa Gwamna Dauda Lawal ne ya rusa hukumar da zarar ya hau.